3 Oktoba 2019 - 06:20
​Iraki: An Kafa Dokar Hana Fita A Birnin Bagadaza

Gwamnatin kasar Iraki ta kafa dokar hana fita a birnin baadaza fadar mulkin kasar da ma wasu birane a kudancin kasar, sakamakon tashe-tashen hankulan da suka wakana.

(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Iraki ta kafa dokar hana fita a birnin baadaza fadar mulkin kasar da ma wasu birane a kudancin kasar, sakamakon tashe-tashen hankulan da suka wakana.

A cikin wani bayani da ofishin firayi ministan kasar ta Iraki ya fitar, Firayi ministan kasar Adel Abdulmahdi ya sanar da kafa dokar han fitaa birnin Bgadaza da wasu birane a kudancin kasar, biyo bayan zanga-zangar da aka yi wadda ta jawo asarar rayuka.

Bayanin ya ce bisa la’akari da halin da aka shiga a cikin kwanaki biyu da suka gabata sakamakon zanga-zangar da aka yi, da kuma yadda ta koma tashin hankali, a kan haka an kafa dokar hana fita a birnin na Bagadaza da sauran biranan da abin ya shafa.

A daya bangaren kuma kwamitin tsaron kasa a kasar ta Iraki ya gudanar da zaman gaggawa a jiya, domin yin dubi kana bin da yake faruwa, inda ya tabbatar da hakkin jama’a na gudanar da jerin gwano cikin lumana, amma ba tare da cutar da jama’a da kuma lalata kaddarorinsu da na gwamnati ba.

Masu gudanar da zanga-zangar dai suna korafi ne kan matsalolin rayuwa da kuma rashin ayyukan yi ga matasa a kasar.



/129